18 Janairu 2020 - 16:04
Harin Iran Ya Jikkata Sojojin Amurka 11

Gwamnatin kasar Amurka ta tabbatar da jikkatar sojojnta 11 a harin da Iran ta kaddamar kan kansaninsu da ke Iraki.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito cewa; Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, mai Magana da yawun cibiyar kula da ayyukan rundunar sojojin Amurka ya bayyana cewa, sojojin Amurka 11 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren da Iran ta kaddamar a kan sansanin sojin Amurka a Iraki.

Ya ce an dauki 8 daga cikin dakarun da suka samu raunuka zuwa kasar Jamus domin yi musu magani, yayin da 3 daga cikinsu suna nan a asisbitin sansanin sojin Amurka na Arifjan da ke Kuwait ana kula da su.

Kakakin ma’aikatar tsarin kasar Amurka ta Pentagon ya bayyana cewa, bayan da sakataren tsaron kasar ta Amurka ya samu bayani kan adadin sojojin Amurka da suka jikkata a wannan hari, ya bayar da umarnin kai asibitotin na Jamus da kuma Kuwait domin samun kula.

Harin martanin na Iran kan sansanin sojin na Amurka da Ainul Asad a Iraki, ya yi sanadiyyar rusa wasu daga cikin manyan kayan yakin Amurka da suka hada har da jirage masu saukar angulu na yaki.